Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
NPC za ta tattauna daftarin shawarar jinkirta taronta na shekara-shekara
2020-02-17 20:09:40        cri
Zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin(NPC) zai gana a karshen watan Fabrairu, don tattauna daftarin shawarar jinkirta taronsa na shekara-shekara.

Mai magana da yawun hukumar kula da harkokin majalisar ta NPC Zang Tiewei shi ne ya bayyana haka ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin yiwuwar daukar wannan mataki. Ya ce, an gabatar da wannan shawara ce, yayin da shugabannin zaunannen kwamitin majalisar ta NPC suka gana Litinin din nan.

A baya dai an shirya bude taron shekara-shekara na majalisar na uku karo na 13 ne a ranar 5 ga watan Maris a birnin Beijing, har ma shirye-shirye sun yi nisa. Amma bayan barkewar cutar numfashin ta COVID-19, matakan kandagarki da hana yaduwar cutar sun kasance aiki mafi muhimmanci a halin yanzu. Sannan yanzu ana cikin muhimmin lokaci na hana yaduwa da ma ganin bayan wannan cuta, don haka, dole a kara himma.

Kimanin wakilai 3,000, ciki har da manyan jami'ai a matakan birane da larduna da sauran fannoni na kan gaba a aikin yaki da wannan cuta. A saboda haka, bayan nazari mai zurfi, hukumar shugabannin, ta yanke shawarar cewa, ya zama wajibi a dage taron shekara-shekara na majalisar, don mayar da hankali kan yaki da wannan annoba. Hakan ya dace da ba da muhimmanci ga tsaro da lafiyar jama'a a matsayin abu mafi muhimmanci.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China