Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Lardin Hubei ya ba da rahoton sabbin mutane 4,823 da suka kamu da cutar
2020-02-14 10:04:55        cri

Hukumar lafiya ta lardin Hubei dake yankin tsakiyar kasar Sin, inda cutar numfashi da kwayar cutar Corona ke haddasawa ta bulla, ta bayyana sabbin mutane 4,823 da suka kamu da cutar kana mutane 116 suka mutu sanadiyar cutar.

Sabbin alkaluman sun hada da mutane 3,095 da aka yi musu binciken kimiya, aka kuma tabbatar suna dauke da cutar. Sabbin wadanda suka mutu sun hada da mutane takwas da su ma aka yi musu bincke. Sabon rahoton ya nuna yawan mutane 51,986 da aka tabbatar sun kamu da cutar a lardin da wannan annoba ta fi kamari.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China