Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar sojan Sin ta kara tura ma'aikatan lafiya 2,600 zuwa birnin Wuhan
2020-02-13 15:37:36        cri
Yau Alhamis, rundunar sojan Sin ta kara tura ma'aikatan lafiya 2,600 zuwa birnin Wuhan domin ba da taimako wajen yaki da cutar numfashi ta Corona. Ana sa ran ganin ma'aikatan da aka tura su gudanar da aikin jinya a asibitin Tai'kang'tong'ji na birnin Wuhan da asibitin kula da yara da mata na lardin Hubei dake yankin Guanggu, bisa tsarin ba da jinya na asibitin Huo'shen'shan.

Haka kuma, bi da bi ma'aikatan lafiyar rundunar soja za a rarraba su a asibitocin birnin. Yau ne kuma rukuni na farko mai kunshe da mutane 1,400 zai isa birnin Wuhan, inda za su fara aiki da zarar sun isa birnin.

Tun lokacin da annobar ta barke ya zuwa yanzu, rundunar sojan Sin ta tura rukumomi guda uku da suka kunshi sama da ma'aikatan lafiya dubu 4 zuwa birnin Wuhan domin ba da taimako wajen yaki da wannan annoba. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China