Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya tattauna ta wayar tarho da firaministan Malaysiya game da cutar numfashi
2020-02-14 10:40:11        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna da firaministan kasar Malaysiya Mahathir Mohamad ta wayar tarho a ranar Alhamis, inda dukkan bangarorin biyu suka bayyana kwarin gwiwarsu na cimma nasarar yakin da annobar cutar numfashi ta novel coronavirus da kasar Sin ke yi.

Xi ya ce tun bayan da annobar novel coronavirus ta barke, gwamnatin kasar Sin ta mayar da hankalinta matuka kan halin da ake ciki, ta fadakar da dukkan jama'ar kasar, al'ummar kasar sun hada kai a matsayin tsintsiya madaurinki daya kuma sun dauki matakai na bai daya, domin kandagarki da kuma dakile yaduwar cutar.

Xi ya ce, namijin kokarin da kasar Sin take yi ya haifar da kyakkyawan sakamako, adadin barnar da annobar ke yi yana raguwa, ana ci gaba da aikin kula da lafiyar wadanda suka kamu da annobar, kuma yawan mutanen da suke warkewa daga cutar yana kara yawa matuka.

Shugaba Xi ya ce gwamnatin kasar Sin tana ci gaba da karfafawa al'ummar Sinawa gwiwa, domin su yi aiki tare da juna, su dauki matakai na zamani wajen kandagarki da kuma dakile annobar, su yi amfani da muhimman dabaru, domin cimma nasarar kawar da annobar baki daya.

A madadin al'ummar kasar Malaysiya, Mahathir ya jajantawa gwamnatin kasar Sin, da al'ummar kasar, bisa ga ibtila'in barkewar annobar cutar ta novel coronavirus.

Mahathir ya ce kasar Malaysian ta gamsu matuka bisa yadda kasar Sin ta himmatu da irin nasarorin da aka cimma a yaki da annobar, kana ya bayyana wannan matakin da cewa tamkar wata gudunmowa ce da kasar ke bayarwa wajen tabbatar da tsaron al'ummar duniya baki daya.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China