Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sabbin wadanda suka kamu da cutar coronavirus sun kai 15,152
2020-02-13 19:55:59        cri
Mahukuntan lafiya a kasar Sin, sun ce sabbin wadanda suka kamu da cutar coronavirus a ranar Laraba, sun kai mutum 15,152, yayin da yawan wadanda cutar ta hallaka suka kai mutum 254, a yankunan lardunan kasar 31, da kuma rukunin sojoji ma'aikata masu bada taimako a jihar Xinjiang.

A cewar kakakin hukumar lafiya ta kasar Sin Mi Feng, cikin wadanda suka rasu, mutum 242 'yan lardin Hubei ne. Sai kuma mutane 2 daga lardin Henan, da mutane daidai daga lardunan Tianjin, da Hebei, da Liaoning, da Heilongjiang, da Anhui. Sauran lardunan sun hada da Shandong, da Guangdong, da Guangxi, da Hainan, da Xinjiang. A dai jiya Laraban, an samu karin mutane 2,807 da ake tantancewa domin sanin matsayinsu game da cutar.

A daya bangaren kuma, adadin wadanda suke cikin matsanancin yanayin rashin lafiya sun ragu zuwa mutum 174, yayin da kuma aka sallami mutum 1,171 daga asibiti, bayan sun samu waraka. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China