Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Lardin Hubei ya ba da rahoton sabbin mutane 14,840 da suka kamu da COVID-19
2020-02-13 12:48:08        cri
A yau ne hukumar lafiya a lardin Hubei dake tsakiyar kasar Sin, inda annobar numfashi ta COVID-19 ta bulla, ta ba da rahoton sabbin mutane 14,840 da aka tabbatar sun kamu da cutar kana wasu mutane 242 suka mutu a ranar Laraba. Wannan shi ne adadi mafi yawa da aka samu a rana tun bullar wannan annoba.

Hukumar ta ce, adadin sabbin wadanda suka kamu da cutar, ya hada da mutane 13,332 da aka tantance a asibiti aka kuma tabbatar sun kamu da cutar. Gaba daya adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a lardin ya kai 48,206. Ya zuwa ranar Laraba, mutane 1,310 ne cutar ta halaka a lardin.

Alkaluma na nuna cewa, galibin wadanda bincike suka tabbatar sun kamu da cutar, sun fito ne daga lardin Hubei. Ciki har da wadanda cutar ta halaka. A cewar hukumar, duk wadanda ake zaton sun kamu da cutar numfashi bayan gudanar da bincike na kimiyya, ana daukarsu a matsayin wadanda suka kamu da cutar.

Hukumar lafiyar lardin ta kuma bayyana cewa, an sake gudanar da binciken ne, don baiwa wadanda aka gano suna dauke da cutar damar samun magani a kan lokaci , ta yadda za a inganta matakan ba da jinya ga wadanda ake kula da su.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China