Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude asibitocin wucin gadi guda 7 a birnin Wuhan
2020-02-13 12:10:41        cri

Rahotanni daga hukumar dake jagorantar matakan kandagarkin cutar numfashi ta birnin Wuhan sun bayyana a jiya Laraba cewa, a halin yanzu, an bude asibitocin wucin gadi guda 7 da cibiyoyin ba da jinya ga wadanda suka kamu da cutar numfashi sama da guda 40, a birnin na Wuhan, lamarin da ya kyautata tsarin ganowa da ba da jinya ga wadanda suka kamu da cutar.

Haka kuma, akwai ma'aikatan lafiya da nas-nas 4,966 dake aiki a wadannan asibitocin wucin gadi guda 7, inda suka fara karbar wadanda suka kamu da cutar numfashi tun daga ranar 6 ga wata, kana ya zuwa karfe 7 na ranar 12 ga wata, gaba daya, an kwantar da wadanda suka kamu da cutar 4,313 a asibitocin da aka tanada.

Bugu da kari, a halin yanzu, akwai cibiyoyin kula da wadanda suka kamu da cutar numfashi sama da guda 40 da aka samar, ciki har da asibitin Huoshenshan da na Leishenshan, gaba daya akwai gadajen kwantar da marasa lafiya guda dubu 12, kuma za a yi amfani da su wajen jinyar marasa lafiya dake cikin yanayi mai tsanani.

Ban da haka kuma, birnin Wuhan ya karfafa aikin binciken dukkan mazauna birnin bisa ka'idar "bincken ko wane gida, da ko wane mutum, da kuma a ko wace rana". Kana, ya zuwa karfe 5 na yammacin ranar 11 ga wata, gaba daya, an tantance magidanta fiye da miliyan 4, ciki har da mutane fiye da miliyan 10. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China