Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta kula da ci gaban tattalin arziki da jin dadin jama'a yayin da take ci gaba da yaki da cutar Corona
2020-02-13 11:16:14        cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya bayyana cewa kasarsa za ta karfafa matakan daidaita tattalin arziki da dawo da aikin kamfanonin samar da kayayyaki da rabawa da samar da muhimman kayayyaki, don daidaita ci gaban jin dadin jama'a da tattalin arziki, a daidai lokacin da kasar take ci gaba daukar matakan yaki da annobar numfashi da ta bulla a kasar.

An bayyana wadannan matakai ne, yayin taron majalisar gudanarwar kasar na ranar Talata da firaminista Li Keqiang ya jagoranta. Taron ya kuma bayyana bukatar karfafawa kamfanonin gwiwar dawo wa bakin aiki bisa tsarin da ya dace. A halin yanzu abu mafi muhimmanci da ya dace ga lardin Hubei shi ne, ya mayar da hankali wajen dakile wannan annoba, yayin da ake kokarin tabbatar da ganin kamfanoni sun dawo da aikin samar da muhimman kayayyakin hana yaduwar cutar da na hidimomi da ake bukata a manyan birane.

Haka kuma an bukaci sauran lardunan kasar, da su dauki managartan matakai na kandagarki da hana yaduwar cutar bisa yanayin da suke ciki. Kana a galibin birane da sauran lardunan dake da karancin wadanda suka kamu da cutar, ya kamata gwamnatocin kananan hukumomi, da su tsara matakan dawo da ayyukan kamfanonin samar da kayayyaki yadda ya kamata.

Taron ya kuma bukaci masu samar da muhimman kayayyakin kiwon lafiya, da su hanzarta dawowa bakin aiki gadan-gadan, don biyan bukatun matakan yaki da wannan annoba. Sannan wajibi ne bangarorin sufuri, da muhimman tashoshin tsare-tsare da gudanar da ayyukansu ba tare da barin jama'a suna taruwa ba. Sannan za a iya dawo da hidimomin jiragen kasa da motocin sufuri na jama'a bisa tsari a wuraren da annobar ba ta yi tsanani ba.

Bugu da kari, taron ya bukaci, rassan gwamnatoci na kasa, da su bullo da matakai na musamman, don taimakawa kamfanoni jure illar bullar wannan annoba, ta yadda za su magance matsalolin da harkokin kasuwancinsu za su fuskanta, musamman kananan kamfanoni da masu zaman kansu. Haka kuma ya kamata a aiwatar da matakai na wucin gadi, don taimakawa harkokin kasuwanci, ciki har da rage ko dauke kudin haya ga kamfanonin gwamnati masu zaman kansu, da rage kudaden haya da inganta manufofin rage kudaden haraji.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China