Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya tattauna ta wayar tarho da sarkin Qatar game da cutar numfashi da ta bulla a kasar
2020-02-12 09:55:11        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna ta wayar tarho jiya da dare da sarkin kasar Qatar Sheikh Tamin bin Hamad Al Thani, inda ya bayyana tabbacin samun nasara a yaki da cutar numfashin da ta bulla a kasar.

Xi ya bayyana cewa, a wannan lokaci mai wahala da kasar Sin ta ke kokarin ganin bayan wannan annoba, kasar Qatar ta sha bayyana kudirinta na nuna goyon baya ga kasar Sin da bude hanyoyin jiragen saman kasar, ta yadda kasar Sin za ta yi jigilar kayayyakin yaki da wannan annoba, kuma kasar Sin ta yaba da ma nuna godiyarta da wannan karamci.

Tun lokacin da wannan annoba ta barke, kasar Sin ta yi kira ga daukacin 'yan kasar, da su hada kai don yaki da wannan cuta, tare da daukar managartan matakan kandagarki da na yaduwar cutar da kaddamar da gangamin 'yan kasa kan yaki da cutar.

Shugaba Xi ya bayyana cewa, yanzu haka an samu gagarumar nasara ta hanyar matakan kandagarki da ma hana yaduwar wannan cuta da aka dauka.

A nasa bangare, sarki Sheikh Tamin, a madadin gwamnati da al'ummar kasarsa, ya bayyana cikakken goyon baya ga gwamnati da al'ummar kasar Sin, a yakin da suke yi da wannan cuta, ya kuma mika sakonsa na ta'aziya ga wadanda cutar ta halaka, tare da jajantawa iyalansu, sannan ya yi fatan samun sauki cikin hanzari ga marasa lafiyan dake kwance.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China