Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yankuna daban-daban na kasar Sin sun fara dawo wa aiki ban da lardin Hubei
2020-02-11 15:29:25        cri
Alkaluman kididdaga da hukumar raya kasa da yin kwaskwarima ta kasar Sin ta fitar a yau Talata na nuna cewa, yankuna daban-daban na kasar Sin sun fara dawo wa bakin aiki sunnu a hankali ban da lardin Hubei, musamman ma a fannin samar da kayayyakin jinya, da makamashi da abinci da jigilar kayayyaki da sauran muhimman fannoni.

A jiya ne, aka kawo karshen hutun bikin bazara da aka tsawaita sakamakon barkewar cutar numfashi, kuma aka fara farfado da ayyuka a wurare daban-daban. A matsayin wani muhimmin bangare a duniya wajen samar da kayayyaki, wadannan kamfanoni sun dawo bakin aiki ta hanyar kula da lafiyar ma'aikatansu da ba da gudunmawarsu ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China