Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: Ba da muhimmanci ga tsaron rayukan jama'a
2020-02-05 20:17:59        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada a yau Laraba a birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, cewar yayin da ake kokarin tinkarar cutar numfashi da ta bullo a kasar, ya kamata dukkan sassan kasar su zama karkashin jagorancin kwamitin tsakiya na jami'iyar Kwaminis ta kasar Sin, inda za a mai da tsaron rayukan jama'a da lafiyarsu a gaban kome. Za a dauki matakai daga bangarorin doka, da aiwatar da su, da kokarin martaba su, ta yadda za a kyautata dabarun hana yaduwar cuta, da daidaita al'amura bisa doka, don tabbatar da gudanar aikin dakile cuta yadda ya kamata.

Shugaba Xi ya yi furucin ne yayin da yake jagorantar taro karo na 3 na kwamitin kula da aikin tabbatar da aiwatar da mulki bisa doka. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China