Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya gana da babban daraktan WHO
2020-01-28 20:27:39        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus yau Talata a Beijing, fadar mulkin kasar.

Yayin zantawar su, shugaba Xi ya ce a halin yanzu, daukacin al'ummar kasarsa na iyakacin kokarinsu, wajen dakile cutar numfashin da kwayar cutar coronavirus ke haddasawa. Ya ce a ko da yaushe, tsaron al'umma, gami da lafiyarsu na gaban komai, kuma aikin da ya kamata gwamnatin kasar Sin ta ba fifiko shi ne daukar matakan kandagarkin yaduwar wannan annobar.

Xi ya ce, shi kansa yana jagorantar wannan aiki, kuma yana da yakinin samun galaba kan yaduwar cutar, ta hanyar karfafa hadin-gwiwa, da daukar matakan da suka dace.

A nasa bangare kuwa, Mista Ghebreyesus cewa ya yi, bayan barkewar cutar, gwamnatin Sin ba ta bata lokaci ba, inda nan take ta gudanar da bincike, da gano ainihin nau'in kwayar cutar, gami da bayyanawa WHO, da sauran kasashe yadda wannan kwayar cutar take. Bugu da kari, gwamnatin kasar Sin na tsayawa tsayin daka wajen daukar managartan matakan dakile yaduwar cutar, wanda hakan ya cancanci yabo. Ya ce matakan da gwamnatin kasar Sin ke dauka, za su taimaka sosai ga kawar da cutar baki daya.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China