Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin ya yi karin haske kan matakan yaki da 'yan ta'adda na ketare
2020-02-12 10:35:30        cri

Wakilin din-din-din na kasar Sin a MDD da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake Vienna, Wang Qun ya gabatar da shawarwari guda hudu kan yadda za a yaki mayakan 'yan ta'adda na ketare. Ya bayyana cewa, ta'addanci babban makiyin bil-Adama ne kuma yaki da wannan matsala nauyi ne da ya rataya a wuyan dukkan kasashen duniya.

Wang Qun ya bayyana haka ne jiya Talata, yayin da yake jawabi a taron manyan jami'ai kan yaki da ta'addanci a yankin Turai da aka gudanar a Vienna, inda ya bayyana muhimmin matsayin kasar Sin kan yaki da ta'addanci.

Ya ce, halin da duniya ke ciki game da yaki da ta'addanci, abu ne mai sarkakiya da kuma damuwa. A cewarsa, ya kamata kasashen duniya, su yi kokarin samar da al'umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adama da hada kai don kawar da barazanar da mayakan 'yan ta'adda na ketare ke haifarwa.

Daga nan sai ya yi karin haske kan shawarwari hudu da ya gabatar, kan yadda za a yaki mayakan 'yan ta'adda na ketare. Na farko amfani da ma'auni na bai daya kan yadda za a matsa musu lamba. Ba za a lamunci yin fuska biyu da zabar yadda za a yaki ta'addanci ba. Na biyu, karfafa hadin gwiwa da daukar matakai ta hakika. Na uku, daukar managartan matakai a dukkan fannoni don magance abubuwan dake haddasa ta'addanci daga tushe. Sai na hudu kuma na karshe, ya kamata MDD da kwamitin sulhu, su taka muhimmiyar rawa bisa jagorancin bangarorin da abin ya shafa.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China