Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta tallafawa kanana da matsakaita kamfanoni yayin da ake fama da barkewar annoba
2020-02-10 10:45:57        cri

Gwamnatin kasar Sin za ta yi samar da tallafin kudade da nufin bunkasa kanana da matsakaitan kamfanonin kasar, bayan dawowarsu daga hutun bikin bazara wanda ya fuskanci matsalar barkewar annobar cutar numfashi ta novel coronavirus.

Cikin wata sanarwar da ma'aikatar kula da masana'antu da sadarwa ta kasar ta fitar ta ce, kananan gwamnatocin biranen kasar za su rage yawan kudaden haraji ga kanana da matsakaitan kamfanonin kuma za'a samar musu da karin rangwame don su samu kwarin gwiwa da kuma saukin gudanar da ayyukansu.

Sanarwar ta ce, hukumomin kula da al'amurran kudi za su gabatar da wani shirin bayar da rance mai karancin kudin ruwa ga kanana da matsakaitan kamfanonin a yankunan da barkewar annobar ta shafa.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China