Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Guterres ya bukaci a bunkasa rayuwar mata
2020-02-10 10:38:28        cri

Kwararru da masu tsara dabarun mulki sun yi kira ga shugabannin kasashen Afrika da su tabbatar da aiwatar da ayyukan bunkasa rayuwar matan nahiyar da 'yan mata yayin da ake kokarin tabbatar da dorewar zaman lafiya.

Ko da yake a shekarar 1995 matan Afrika sun bayyanawa duniya matsalolinsu a lokacin babban taron karawa juna sani na mata na kasa da kasa a Beijing, har yanzu ci gaban da aka samu bai gamsar ba a matsayin bangaren cimma muradun mata karkashin yarjejeniyar Beijing, babban sakataren MDD, Antonio Guterres, ya bayyana hakan ga babban taro game da samar da daidaiton jinsi da ci gaban mata wanda aka gudanar da yammacin ranar Asabar a Addis Ababa na kasar Habasha.

Guterres ya kara da cewa, bisa abin da da ya lura da shi tun yana karamin yaro shi ne, yawancin karfin iko ba'a mika shi, sai dai idan aka nema. Ya ce idan batun yana da nasaba da karfin iko, samun ra'ayoyin bai daya tsakanin bangarorin zartaswa yana da matukar muhimmanci.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China