Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Tattalin Arziki Mai Alaka Da Intanet Na Taimakawa Kokarin Dakile Cutar Numfashi A Kasar Sin
2020-02-02 20:37:52        cri

A sakamakon barkewar cutar numfashi mai saurin yaduwa ta "Novel Coronavirus Infection" a kasar Sin, gwamnatin kasar ta dauki kwararan matakai domin dakile yaduwar annobar, matakan da suka hada da takaita zirga-zirgar mutane, da magance taruwar jama'a. Wannan ya sa a lokacin da ake murnar bikin bazara na gargajiyar kasar Sin, ba a ganin fitowar jama'a da yawa zuwa wasu wuraren sayen kayayyaki, ko dakunan cin abinci, ko kuma wuraren yawon shakatawa ba, kamar yadda aka saba gani a shekarun baya. Wannan lamari ya sa wasu ke nuna damuwa kan yanayin tattalin arzikin kasar Sin a wannan shekara. Amma hakika, ta hanyar tattalin arziki mai alaka da fasahohin intanet, mutane suna aiki, da karutu, gami da sayen kayayyakin da suke bukata, ba tare da fitowa zuwa waje ba. A wannan lokacin da ake fama da cutar numfashi mai yaduwa, tattalin arziki mai alaka da fasahohin intanet na taka muhimmiyar rawa ga kokarin tabbatar da ingancin gudanar harkokin yau da kullum na al'ummun kasar Sin.

Idan mun dauki iyalin Madam Han, wadda ke zama a birnin Beijing na kasar Sin, a matsayin misali. Tun bayan barkewar annobar cutar numfashi, ita Madam Han da iyalinta sun dade suna zamansu a cikin gida. Ta hanyar shafin yanar gizo na intanet, Madam Han ta sayi abinci da kayayyakin masarufi don biyan bukatun mambobin iyalinta. Har ma ta sayi wasu sutura da kayan kawa domin kanta. A nashi bangare, mijin Madam Han yana shafe lokacinsa wajen yin wasanni ta wayar salularsa. Sa'an nan diyarsu tana sauraron darrusan da ake gabatarwa ta shafin intanet, don ci gaba da karatunta a wannan lokaci da ake takaita fitowar mutane.

Bisa duba da yadda iyalin Madam Han suke zaman rayuwa za a iya ganin ci gaban tattalin arziki mai alaka da fasahar intanet a kasar Sin. Alkaluman da aka samu sun nuna cewa, tun daga shekarar 2012 zuwa ta 2018, yawan kudin da tattalin arziki mai alaka da fasahar intanet ya shafa ya karu daga RMB Yuan trillian 11.2 (kwatankwacin dalar Amurka trillian 1.6) zuwa RMB Yuan trillian 31.3 (kwatankwacin dalar Amurka trillian 4.5). Kana darajar tattalin arziki mai alaka da intanet cikin ma'aunin GDPn kasar Sin ya habaka daga kashi 20.8% zuwa kashi 34.8%, wanda ya zama na biyu mafi yawa a duniya.

Yanzu Sinawa na kokarin dakile cutar numfashi mai yaduwa, wadda za ta yi tasiri kan yanayin tattalin arzikin kasar cikin wani gajeren lokaci. Amma ci gaban tattalin arzikin kasar mai alaka da fasahar intanet zai iya saukaka illar da annobar ka iya haifarwa ga tattalin arzikin kasar baki daya. Har yanzu wani yanayi na samun ci gaba mai inganci na tattalin arzikin kasar Sin bai canza ba ko kadan. Hakan ya ba Sinawa kwarin gwiwa wajen dakile cutar numfashi da ci gaba da raya tattalin arziki a kasarsu. (Mai fassarawa: Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China