![]() |
|
2020-01-20 20:21:06 cri |
Bayan abkuwar lamarin, kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin da majalisar gudanarwar kasar sun dora muhimmanci sosai. Inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da umurni cewa, yayin bikin bazara ke karatowa, an kara samun zirga-zirgar jama'a a kasar Sin, don haka yana da muhimmanci sosai a kara zage damtse wajen yaki tare da magance bazuwar cutar a kasar. Ya ce kamata ya yi kwamitocin jam'iyyar kwaminis ta Sin da gwamnatocin wurare daban daban su kara mai da hankali kan lafiyar jama'a, da tsara shirye-shiryen yaki da magance bazuwar cutar, da daukar matakai don hana bazuwar cutar. Haka kuma ya kamata a ba da jinya ga wadanda suka kamu da cutar, da yin bincike kan dalilin bullor cutar, da kara sa ido kan mutanen da suka kamu da cutar, da kuma gudanar da ayyuka bisa ka'idoji. Haka, ya kamata a gabatar da rahoto game da yawan mutanen da suka kamu da cutar cikin lokaci, da kara yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da sauran kasashe kan wannan batu. (Zainab)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China