Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta sanar da sabbin mutane 3,062 da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi
2020-02-10 09:55:35        cri

Hukumomin lafiyar kasar Sin sun sanar a yau Litinin cewa an samu rahoton sabbin mutane 3,062 sun kamu da annobar cutar numfashi ta novel coronavirus yayin da yawan sabbin mutanen da suka mutu ya kai 97 a ranar Lahadi daga larduna 31 na kasar da yankin aikin sojoji na Xinjiang.

Daga cikin wadanda suka mutu, 91 daga lardin Hubei ne, sai mutane biyu daga lardin Anhui, sai mutum guda daga lardunan Heilongjiang, Jiangxi, Hainan da kuma lardin Gansu, a cewar hukumar kula da lafiya ta kasar Sin.

Hukumar lafiyar ta ce an kuma samu sabbin mutane 4,008 da ake zaton sun kamu da cutar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China