Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An sallami marasa lafiya 3,281 da suka warke daga cutar Corona daga asibitoci daban-daban a kasar Sin
2020-02-10 09:18:27        cri

Hukumomin lafiya a kasar Sin sun sanar a yau Litinin cewa, an sallami jimillar marasa lafiya 3,281 jiya Lahadi daga asibitoci daban-daban a kasar Sin, bayan sun warke daga cutar numfashi ta Corona da ta bulla a kasar.

Hukumar lafiya ta kasar Sin ta bayyana haka ne, a rahoton da ta saba fitarwa a ko wace rana, tana mai cewa, jiya Lahadi, an sallami mutane 632 daga asibiti bayan an tabbatar sun warke daga wannan cuta, ciki har da mutane 356 a lardin Hubei. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China