Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan lafiya na Kamaru ya yaba gudummawar da tawagar maaikatan lafiyar kasar Sin ta bayar a kasar
2019-12-03 14:26:51        cri

Ministan lafiya na kasar Kamaru Malachie Manaouda ya bayyana cewa, gagarumar gudummawar da tawagar ma'aikatan lafiyar kasar Sin ta bayar a kasar, tana ci gaba da inganta yanayin kiwon lafiyar kasar, matakin da ministan ya bayyana a matsayin aboka na alkawari tsakanin kasashen biyu.

Manaouda ya bayyana haka ne, yayin bikin ban kwana da aka shiryawa tawagar ma'aikatan lafiyar kasar Sin ta 19 tare da maraba da tawaga ta 20.

Ministan ya ce, likitocin kasar Sin sun ba da muhimmiyar gudummawa wajen kula da lafiyar al'umomin kasar Kamaru da ma koyar da ma'aikatan lafiyar kasar dabarun kiwon lafiya.

A nasa jawabin jakadan kasar Sin dake kasar Kamaru, Wang Yingwu, ya bayyana cewa, a shirye bangaren kasar Sin yake ya kara zurfafa alaka da bangaren Kamaru a bangaren kula da jama'ar jama'a, ta yadda za a aiwatar da matakan kiwon lafiya cikin manyan matakan da aka tsara yayin taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka(FOCAC) da ya gudana a birnin Beijing a shekarar 2018.

A lokacin da tawagar ma'aikatan lafiya ta kasar Sin ta 19 ke gudanar da aikinta na shekara daya a kasar ta Kamaru, ta samar wa sama da marasa lafiya 25,000 magani, da yin aikin tiyata sama da 500, sannan ta yi tafiye-tafiye sau 9 don samar da magani da hudima kyauta ga mutane masu rauni dake zaune a yankunan karkarar kasar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China