2020-01-15 23:10:03 cri |
A yau Laraba ne firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya jaddada muhimmancin tsarin salon kasuwa mai nagarta, da tanajin dokoki da za su dace da yanayin ci gaban kasuwanci a mizanin kasa da kasa.
Li Keqiang, ya bayyana hakan ne yayin wani taron musayar ra'ayi da ya gudana a wannan rana, inda ya saurari mahangar kwararru, da masana, da 'yan kasuwa, da ma shawarwarin su game da rahoton aikin gwamnati. Li Keqiang ya ce ya zama wajibi a gaggauta gina yanayin kasuwanni, wadanda za su dace da mizanin kasa da kasa, da samar da dokoki, ta yadda za a ba masu ruwa da tsaki kwarin gwiwa.
Taron dai ya samu halartar kwararru, da masana daga cibiyoyin ilimi da bincike daban daban, ciki hadda cibiyar kimiyyar zamantakewar al'umma ta kasar, da na jami'ar Renmin, da sauran cibiyoyin manyan kwalejojin kasar, da jagororin kamfanonin da suka hada da kamfanin fasahar sadarwa na Xiaomi. (Saminu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China