Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban jami'in MDD ya yabawa rundunar kasar Sin dake wanzar da zaman lafiya a Darfur
2020-02-08 18:38:16        cri
Laftanar janar Carlos Humberto Loitey, mashawarcin babban magatakardan MDD a fannin aikin soja, ya yi rangadi a sansanin sojojin kasar Sin dake aikin wanzar da zaman lafiya a yankin Darfur na kasar Sudan, a jiya Jumma'a, inda ya yaba wa sojojin kan yadda suke bin umarni, da nuna kwarewa a fannoni daban daban, gami da sauke nauyin dake wuyansu yadda ya kamata.

Laftanar janar Carlos Loitey, ya yi wannan rangadi ne don tantance yanayin da ake ciki a kokarin kafa hadaddiyar rundunar wanzar da zaman lafiya ta MDD da ta kungiyar tarayyar Afirka AU.

Rundunar ta kasar Sin dake yankin Darfur, ta kunshi sojojin injiniya da kuma masu tuka jiragen sama masu saukar ungulu, wadanda ke taka muhimmiyar rawa a kokarin kiyaye zaman lafiya a yankin. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China