Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin ya gana da firaministan kasar Cambodia
2020-02-05 21:02:48        cri
A yau Laraba, shugaban kasar Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Cambodia Samdech Hun Sen a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Yayin ganawarsu, shugaba Xi Jinping ya ce kasar Sin na da cikakken imani, da fasahohi wajen dakile cutar numfashi mai yaduwa ta Corona. A nasa jawabin firaminista Hun Sen ya ce, ya zo kasar Sin a wannan lokaci ne, domin nuna wa gwamnatin kasar Sin da jama'arta cikakken goyon baya, a madadin gwamnati da jama'ar kasar Cambodia. Firaministan na Cambodina ya ce, kasarsa za ta ci gaba da hadin gwiwa da mu'amala da kasar Sin, da kokarin raya al'umma mai kyakkyawar makomar bai daya ta kasashen Cambodia da kasar Sin. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China