Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya aike da sakon murnar cika shekaru 20 da kafa dandalin FOCAC
2020-02-05 19:17:48        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aikawa takwaransa na kasar Senegal Macky Salla, kana shugaban dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) wasika, don taya dandalin murnar cika shekaru 20 da kafuwa.

A cikin wasikar, shugaba Xi ya jaddada cewa, a shirye kasar Sin take ta hada kai da Senegal don sauke nauyin shugabancin dandalin da amfani da damar bikin cika shekaru 20 da kafuwar dandalin wajen hada kai da kasashen Afirka, ta yadda za a aiwatar da sakamakon taron kolin dandalin na Beijing yadda ya kamata, da sa kaimi ga bunkasa alakar Sin da Afirka bisa manyan tsare-tsare da gina al'umma mai kyakkyawar makoma tsakanin Sin da Afirka. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China