Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Geng Shuang: ziyarar ministan harkokin wajen Sin a Afirka duk farkon shekara na nuni ga dankon zumunta ta musamman tsakaninsu
2020-01-14 20:24:48        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya ce cikin shekaru 30 kawo yanzu, ziyarar da ministan harkokin wajen Sin ke gudanarwa a wasu daga kasashen nahiyar Afirka a duk farkon shekara, na nuni ga dankon alaka ta musamman dake tsakanin Sin da Afirka.

Geng Shuang ya bayyana hakan ne a Talatar nan, yayin taron manema labarai da aka gudanar a nan birnin Beijing. Ya ce tsakanin ranekun 7 zuwa 13 ga watan Janairun nan, dan majalissar gudanarwa, kuma ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya ziyarci kasashen Masar, da Djibouti, da Eritrea, da Burundi da Zimbabwe.

Kaza lika a yayin wannan ziyara, Wang Yi da wasu shugabannin nahiyar, da takwarorin aikin sa na kasashen da ya ziyarta, sun yi musaya mai zurfi, tare da cimma matsaya guda a fannin yaukaka alakar su, da zurfafa hadin gwiwar cimma moriya tare. Ya ce dukkanin sassan biyu sun bayyana burin su na gaggauta aiwatar da sakamakon dandalin FOCAC da ya gabata na birnin Beijing, tare da ingiza hadin gwiwar aiwatar da manufofin dake kunshe cikin shawarar "ziri daya da hanya daya ", da kara hada karfi wajen aiwatar da hadin gwiwar su daga dukkanin fannoni. Dukkanin sassan dai na ganin Sin da Afirka, na cikin wani yanayi na kyawun dangantaka, yayin da makomar hadin gwiwar su ke kara haskawa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China