Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Falasdinawa sun yi Allah wadai da kalaman Amurka game da mamayar Isra'ila
2019-11-19 10:20:05        cri
Al'ummar Falastinawa sun yi Allah wadai da kalaman sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, wanda ya furta cewa mamayar da Yahudawa ke yiwa matsugunan Falastinawa a yammacin kogin Jordan bai saba dokokin kasa da kasa ba.

Cikin sanarwar da aka baiwa manema labarai, kakakin ofishin shugaban Palastinawa Nabil Abu Rudeineh ya ce, kalaman Pompeo abin Allah wadai ne, ba za'a yarda dashi ba, abin jefarwa ne, kuma sun ci karo da dokakin kasa da kasa.

Ya ce Amurka ta riga ta zubar da kimarta baki daya kuma babu wata rawa da zata sake takawa game da batun shirin samar da zaman lafiya.

Haka zalika, kungiyar gwagwarmaya ta Hamas, wacce ke shugabancin zirin Gaza tun a shekarar 2007, ta yi kakkausar suka kan kalaman na Pompeo wanda ya nemi halattawa Yahudawa matsugunan dake yammacin kogin Jordan.

Hamas ta ce, kalaman mista Pompeo manufofi ne da gwamnatin Amurka ke cigaba da aiwatar da su, wacce a koda yaushe take nuna rashin adalci, tana goyon bayan mamayar da ake yi kuma tana cigaba da nuna goyon baya kan cin zarafi da cin zalin da ake yiwa al'ummar Falastinawa. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China