Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Isra'ila ta amince da daukar matakan soja ga kasar Iraki
2019-12-26 10:58:09        cri
A jiya ne, bangaren soja na kasar Isra'ila ya tabbatar karo na farko da cewa, kasar Isra'ila ta taba daukar matakan soja kan kasar Iraki don hana jigilar makaman Iran dake ratsa Iraki zuwa abokan gaba na Isra'ila.

Hafsan hafsoshin sojojin kasar Isra'Ia Aviv Kohavi ya bayyana a gun taron kiyaye tsaro da aka gudanar a birnin Tel Aviv a jiya cewa, ana samun yakin basasa a kasar Iraki, sojojin Quds dake karkashin jagorancin sojojin Islamic na kasar Iran sun yi sumogar makamai a kasar Iraki. Don hana abokan gaba na kasar Isra'ila su samu wadannan makamai, kasar Isra'ila tana daukar matakan soja kan kasar Iraki.

A watan Yuli da Agustan bana, an kai hare-hare ga sansanonin dakarun Shi'a na kasar Iraki da wuraren ajiye makamansu, da kuma sansanin kasar Iran da kungiyar Hezbollah ta Lebanon dake kasar Iraki. A ganin kafofin watsa labaru na Iraki da na Isra'ila, bangaren soja na kasar Isra'ila yana da nasaba da batun.

Bangaren Isra'ila bai taba tabbatar da kai harin sama kan kasar Iraki a fili ba. Amma jami'an kasar sun bayyana sau da dama cewa, mai yiwuwa ne an kai hari ga wuraren soja na Iran dake kasar Iraki. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China