Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kusan kammala gina sabbin asibitoci 2 a birnin Wuhan
2020-02-02 16:29:01        cri

Wani labarin da aka samu daga birnin Wuhan na kasar Sin, inda ake cikin yanayi mafi tsanani na fama da cutar numfashi ta "Novel Coronavirus Infection", an ce an kusan kammala gina sabbin asibitoci guda 2, masu taken asibitin "Huo'shen'shan" da na "Lei'shen'shan". Za a kawo karshen aikin ginin a yau Lahadi, da kuma ranar Laraba 5 ga wata, sa'an nan za a fara kwantar da wadanda suka kamu da cutar numfashi cikin asibitocin 2 daga gobe Litinin, da kuma ranar Alhamis mai zuwa. Gaba daya za a samu gadaje fiye da 2500 cikin asibitocin 2.

An fara gina asibitin "Huo'shen'shan" a ranar 23 ga watan Janairun da ya gabata. Inda aka ba da wa'adin kwanaki 10 domin kammala aikin gina asibitin. Yayin da asibitin "Lei'shen'shan" an fara gina shi ne a ranar 26 ga watan Janairu, daga bisani an riga an kammala kashi 60% na aikin ginin cikin kwanaki 5 bayan kaddamar da aikin.

Dalilin da ya sa ake samun damar gina asibitocin guda 2 cikin sauri shi ne, domin an yi amfani da fasahohi mafi ci gaba, inda aka hada bangarorin dakuna waje guda, kafin a saka dakunan cikin fili don su samu damar iya daukar masu fama da cutar numfashin nan mai yaduwa da ake kira "Novel Coronavirus Infection". (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China