Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cibiyar IDC ta yi hasashen rabin GDPn kasar Sin zuwa 2023 zai fito ne daga fannonin fasahar zamani
2019-12-11 15:39:11        cri
Cibiyar IDC mai bincike da fashin baki a fannin hada hadar kasuwannin duniya, ta ce kimanin kaso 51.3 bisa dari na GDPn kasar Sin nan da shekarar 2023 zai fito ne daga fannonin fasahar zamani, duba da yadda kasar ke kara kaimi wajen dora harkokin cinikayya kan na'urorin zamani.

IDC ta yi hasashen cewa, ya zuwa shekarar 2025, a kalla kaso 80 bisa dari na sabbin kamfanonin kasar Sin da za a kafa, za su rika amfani ne da fasahohi masu nasaba da kwaikwayon tunanin bil Adama.

Cibiyar ta ce ayyukan manyan jami'in yada bayanai na kamfanoni, za su kasance ne a fannonin tsara ci gaba ta hanyar kirkire-kirkire, yayin da kuma bukatar kwararru a fannin tsaron bayanai, da tabbatar da bin kaidar su za ta karu.

A cewar manajan IDC reshen kasar Sin Kitty Fok, Sin na kan hanyar zamanantar da na'urori, a gabar da ake bukatar kamfanonin kasar su dauki matakan tunkarar sauyin dake tafe na cin gajiyar sabbin fasahohin zamani. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China