Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sakataren MDD ya damu kan karuwar zaman dar-dar a yammacin Saharan Afirka
2020-01-13 10:43:53        cri

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya damu kan yadda zaman dar-dar yake kokarin kawo cikas ga gasar tsaren motocin ta Monaco-Dakar da ake yi.

Cikin wata sanarwa da kakakinsa Stephane Dujarric ya rabawa maname labarai, Antonio Guterres ya ce ya damu kan yadda ake kara samun zaman tankiya a yankin yammacin Sahara, yayin da mahalarta tseren ke shirin tsallaka yankin Gueguerat buffer a yau Litinin.

Bayanai na nuna cewa, a halin yanzu yankin yammacin Sahara yana karkashin ikon kasar Morocco. Amma yankin Polisario na neman samun 'yancin kansa. Wannan ya sa, babban sakataren na MDD ke kira ga bangarorin da abin ya shafa a wannan rikici, da su kai zuciya nesa tare da rage rura wutar tashin hankali. Yana mai cewa, ya zama wajibi a bar motocin fararen hula da na 'yan kasuwa su rika kai koma kamar yadda suka saba.

Rahotanni na cewa, yankin Polisario na barazanar kawo cikas ga gasar tseren. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China