Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
António Guterres ya yi kira ga bangarori daban-daban da su yi hakuri da juna
2020-01-07 13:21:23        cri
Jiya Litinin, babban magatakardan MDD António Guterres, ya yi kira ga bangarori daban-daban da su yi hakuri da juna bisa iyakacin kokarinsu, don hana tsanantar halin da ake ciki a duniya, da kuma farfado da shawarwari na kasa da kasa, da maido da hadin kan kasa da kasa.

Mr. Guterres ya zanta da manema labarai a New York, hadkwatar MDD, inda ya bayyana cewa, yanzu ana fuskantar rikicin siyasar wani yanki mafi tsanani a wannan karni, har ta kai yanayin da ake ciki na kara tsananta, kuma babu tabbaci ga hana yaduwar makaman nukiliya. Kuma ya nanata cewa, bai kamata a yi biris da halin ba.

Yace yake-yake na kawowa dukkanin Bil Adama miyagun hasarori kwarai da gaske, hakan ya sa hana barkewar yake-yake, ya zama nauyi dake wuyan daukacin Bil Adama. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China