Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta bukaci Amurka ta daina amfani da batutuwan dake alaka da yankin Tibet wajen tsoma baki cikin harkokinta na cikin gida
2020-01-29 21:38:52        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin, Hua Chunying, ta ce matakin da Amurka ta dauka kan yankin Tibet, ya keta dokokin da ka'idojin huldar kasa da kasa, sannan tsoma baki ne cikin harkokin cikin gidan Sin. Haka zalika, ya aike da bahaguwar sako kan batun 'yancin kan Tibet'. Inda ta ce, kasar Sin ya fusata, kuma ta na adawa da matakin.

Da yammacin jiya Talata ne majalisar wakilan Amurka ta yi muhawara tare da zartar da doka kan yankin Tibet.

Hua Chunying, ta jadadda cewa, cikin sama da shekaru 60 da suka gabata, an samu gagarumin ci gaba da kuma sauyi a fannonin tattalin arziki da zaman takewa da al'adu da muhallin halittu a Tibet. A yanzu kuma, tattalin arzikin yankin na ci gaba da habaka, sannan ana zaman lafiya a yankin, baya ga rayuwar jama'a dake kara ingantuwa.

Ta ce batutuwan da suka shafi Tibet, ba batutuwa ne na kasa ko addini ko hakkin dan Adam ba, muhimman batutuwa ne da suka shafi cikakken iko da 'yancin kasar Sin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China