Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana samun hidimomin likitancin gargajiya na Tibet a kaso 89 na asibitocin dake biranen yankin
2019-08-21 11:01:59        cri

Ana samun hidimomin likitancin gargajiya na Tibet a kaso 89 na asibitocin dake biranen yankin Tibet na kasar Sin mai cin gashin kansa.

A cewar wani taron nazari da ya gudana jiya, alkaluma sun nuna cewa a yanzu, Tibet na da asibitoci gwamnati dake bada hidimomin likitancin gargajiya na yankin guda 43 da kuma asibitoci masu zaman kansu 13 dake bada irin hidimar.

Tibet ta gudanar da tarukan yayata likitancin gargajiya na yankin har sau 3, inda kuma take gabatar da jerin dabaru da shirye-shirye a karshe, tare da ware wasu kudi na inganta bangaren a kowacce shekara.

Zuwa karshen shekarar 2018, adadin wadanda suka nemi kulawar likitancin gargajiya na Tibet ya kai miliyan 3.29 a yankin, inda kuma ake da likitocin gargajiya masu rejista sama da 3,700. (Fa'iza Msutapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China