Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumomin kiwon lafiya na kasar Sin sun kira taron baiwa yankin Tibet tallafi ta Intanet
2019-09-18 11:18:59        cri

Jiya Talata, hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin ta kira taron sassan kiwon lafiya na kasar don baiwa yankin Tibet tallafi. Yayin taron, ana ganin cewa, aikin tallafawa yankin Tibet ta fuskar kiwon lafiya ya kyautata yanayin jiyya da kiwon lafiya na wurin da warware matsalar karancin samun jiyya da ma matsalar kudin jiyya.

Ya zuwa yanzu, tsarin kiwon lafiya a yankin ya inganta, har ana ba da hidimmar jiyya mai inganci. An bayyana cewa, yawan mutuwar jarirai a yankin ya ragu zuwa kashi 11.59 cikin dubu daga kashi 16.81 cikin dubu a shekarar 2014, kana yawan mutuwar mata masu juna biyu ya ragu zuwa kashi 56.52 cikin dubu 100 daga kashi 108.86 cikin dubu 100 a shekarar 2014, yayin da yawan mata masu juna biyu da suka haihu a asitibi ya karu zuwa kashi 90.66 cikin dari daga kashi 85.01 cikin dari a shekarar 2014, ban da wannan kuma, yawan matsakaicin shekarun haihuwa a yankinya kai 70.6, al'umma na kara gamsuwa da harkokin jiyya, matakin da ya sa lafiyar jama'a ke kara inganta sosai. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China