Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kulla yarjeniyoyin taimakawa jihar Tibet 202, wadanda kudinsu ya kai RMB Yuan biliyan 21.5
2019-06-18 11:15:33        cri

An kira taron sa kaimi ga kawar da talauci a wuraren da suke fi fama da talauci a jihar Tibet ta kasar Sin, da kuma kara ba da taimako ga aikin kawar da talauci a jihar, a jiya Lahadi a birnin Nyingchi na jihar Tibet. Inda aka kulla yarjeniyoyin taimakawa jihar har 202, wadanda suka shafi fannin sana'o'i daban-daban, da sha'anin ba da ilmi, ba da jiyya, samar da guraben aikin yi, kawar da talauci ta hanyar saye-saye, da kuma kawar da talauci ta hanyar kimiyya. Sannan za a zuba jarin da yawansa ya kai kimanin RMB Yuan biliyan 21.5 ga wadannan ayyuka, matakin da ya sa yawan yarjeniyoyin da aka kulla da kudin da za a kashe wajen kawar da talauci ya kai sabon matsayi.

Tun lokacin da aka fara aikin yaki da talauci, yawan matalauta a jihar ya ragu zuwa dubu 150 daga dubu 590, sannan yawan gundumomi dake fama da talauci ya ragu zuwa 19 daga 74, adadin da ya kai matsayi na farko a kasar Sin a wannan fanni. Kana yawan mutanen da suke fama da talauci ya ragu da kashi 5.6 cikin dari daga kashi 25.2 cikin dari.

An ce, jihar Tibet ta yi niyyar kawar da talauci gaba daya a wannan shekara, ta yadda matalauta dubu 150 da gundumomi 19 dake fama da talauci za su fita daga mawuyacin halin da suke ciki. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China