Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mamban majalisar gudanarwar Sin ya gana da shugaban Kenya
2019-12-18 14:10:36        cri
A ranar 16 ga wata, shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya gana da mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, mista Wang Yong, wanda ke ziyara a kasar da kuma halartar bikin soma aikin titin zirga-zirgar jiragen kasa a tsakanin Nairobi da Malaba na mataki na farko a matsayinsa na manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping.

A yayin ganawar, da farko Wang Yong ya isar da gaisuwa da fatan alheri da shugaba Xi Jinping ya aikowa shugaba Kenyatta, ya kara bayyana cewa, dangantakar dake tsakanin Sin da Kenya na cikin wani lokaci mafi kyau a tarihi, wadda ta kasance abin koyi a hadin kan dake tsakanin Sin da kasashen Afirka. Ya kuma bayyana imanin cewa, a bisa jagorancin shugabannin kasashen biyu, za a ciyar da dangantakar abokantaka ta hadin kai bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni gaba, don kara samar da alheri ga jama'ar kasashen biyu da ma jama'ar nahiyar Afirka baki daya.

A nasa bangare, shugaba Kenyatta ya bayyana cewa, kasarsa na dora muhimmanci sosai kan zumuncin dake tsakaninta da Sin. A cikin shekaru 56 da kasar ta samu 'yancin kai, kasar Kenya ta samu moriya sosai a hadin kan dake tsakaninta da Sin a fannoni daban daban. Kasar Kenya kuma na fatan karfafa wannan dangantakar da Sin, da zurfafa hadin kai a tsakanin bangarorin biyu a fannonin manyan kayayyakin more rayuwar jama'a da cinikayya da zuba jari da dai sauransu, don samun nasara tare. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China