Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kammala aikin samar da talabijin na zamani masu amfani da tauraron dan adam a kauyukan Kenya
2019-12-21 16:54:50        cri

 

 

Jiya Juma'a, an gudanar da bikin kammala aikin samar da talabijin na zamani masu amfani da tauraron dan adam ga kauyukan Kenya a firamare Kinyanjui dake Nairobi, fadar mulkin kasar. Abin da ya nuna cewa, iyalai sama da dubu 16 a kauyuka fiye da 800 za su samu damar amfani da talabijin na zamani masu amfani da tauraron dan adam ba tare da biyan kudi ba.

Wannan aikin yana daga cikin jerin matakan hadin kai ta fuskar al'adu da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a taron koli na Johannesburg na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika na shekarar 2015, da zummar samar da talabijin na zamani masu amfani da tauraron dan adam ga kauyuka fiye da dubu 10 na kasashen Afrika sama da 30. Kenya na daya daga cikin rukunin farko na kasashen da za su ci gajiyar shirin da Sin za ta baiwa taimako. Har ila yau, daga hedkwatar kasar Nairobi zuwa kauye dake tsibiri mai nisa, kauyukan da yawansa ya kai fiye da 800 sun samu talabijin na zamani masu amfani da tauraron dan adam.

Jami'in ma'aikatar sadarwa da kimiyya na kasar Kenya, Hesbon Malweyi ya bayyana cewa, Kenya sahihiyar abokiya ce ga kasar Sin, Sin tana goyon bayan kasar a fannonin daban-daban wajen samun bunkasuwarta, daga cikinsu rediyo da telibjin sabon fanni ne da Sin take bada taimako. Ya kara da cewa, wannan aiki da Sin ta gudanar a kasar ya baiwa jama'ar kasar damar kallon shirye-shiryen telibijin na gida da waje, har wasu kauyuka masu nisa na cin gajiya. Matakin da ya rage gibin dake tsakanin birane da kauyuka a wannan fanni a kasar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China