Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi gwajin bikin murnar sabuwar shekarar kasar Sin ta 2020 karo na 5
2020-01-23 10:35:34        cri

A jiya Laraba ne aka yi gwajin bikin murnar sabuwar shekarar kasar Sin na shekarar 2020, bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin karo na 5, wanda CMG ya gudanar.

An gudanar da aikin gwajin ne a matsayin kari kan gwaji har karo 4 da aka yi a baya, a matsayin matakin share fagen bikin yadda ya kamata, don gabatar da wannan gagarumin biki a lokacin.

Bikin na wannan karo, na kunshe da wasan tattaunawa cikin raha, da wasannin kwaikwayo da dama, abubuwan da suka samu karbuwa sosai wajen jama'a. Wasu kalmomi da jimloli da aka yi amfani da su, sun shahara sosai a nan kasar Sin a shekarar 2019, har ma masu kallo sun nuna cewa, wadannan shirye-shirye na ban dariya, sun haifar da farin ciki sosai. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China