Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gudanar da atisayen gwaji na biyu na bikin murnar ranar bikin bazara
2020-01-17 19:44:17        cri

 

A jiya Alhamis ne babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG a takaice, ya gudanar da atisaye gwaji na biyu, game da bikin murnar ranar bikin bazara ta shekarar 2020.

Mashirya gwajin sun bayyana cewa, a yayin bikin murnar ranar bikin bazara na bana, za a ci gaba da dora muhimmanci kan bayyana rayuwar jama'a, da halin al'ummar kabilu daban daban, da al'adu, da murna da walwala, da harkokin zamanin da muke ciki, da dai sauransu.

Kaza lika an kirkiro sabbin abubuwa a fannonin zane-zanen dandalin wasan kwaikwayo, da tsare-tsaren shirye-shirye, da sauransu. Sauran sun kunshi amfani da sabbin fasahohi, da hada kai wajen amfani da yanar gizo, da talabijin, da sauran hanyoyin watsa labaru da dai sauransu. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China