Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kafofin yada labarai na kasa da kasa za su watsa bikin murnar sabuwar shekara ta 2020 da CMG zai gabatar
2020-01-20 10:13:29        cri

Babban rukunin gidan rediyon da telibijin na kasar Sin CMG, zai gabatar da gaggarumin bikin murnar sabuwar shekara ta 2020 bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin wato shekarar Bera, a daren ranar 24 ga watan da muke ciki. Shirye-shirye masu ban sha'awa da kimiya da fasaha na zamani da za a yi amfani da su a bikin ya jawo hankulan kasa da kasa. Alkaluman da aka bayar na nuna cewa, kafofin yada labarai kimanin 460 daga kasashe ko yankuna daban-daban na duniya 170, za su watsa wannan biki mai armashi.

 

An yi kiyasin cewa, dubban gidajen rediyo da dandalolin watsa labarai bisa fasahohi na zamani da gidajen sinima, za su watsa labarai dangane da wannan kasaitaccen biki. Daga cikinsu kuma, kafofin yada labarai kimanin 280 daga Amurka, da Birtaniya, da Japan da Brazail da kuma Singapore da hadaddiyar daular Larabawa UAE da Malaysia da Tailand da Laos, za su watsa shirye-shiryen bikin. Dadin dadawa, gidajen sinima da telibjin kimanin 20 daga Italiya da Austriliya da UAE da kuma Masar da Indiya da sauransu za su watsa bikin cikin harsuna daban-daban.

 

Wannan biki dai, gaggarumi ne dake nuna al'adun da kowane Basine ba zai iya rabuwa da shi ba a lokacin sabuwar shekara yayin suka hadu da iyalansu. CMG ta fara shiryawa da gabatar da wannan biki ne a kowace shekara a cikin shekaru 30 ko fiye da suka gabata, tun daga shekarar 1983, hakan ya sa kungiya mai rajistar sabon matsayin bajintar duniya ta Guinness, ta shaida cewa, bikin murnar sabuwar shekara ta kasar Sin, ya zama shirin telibijin dake da masu kallo mafi yawa a duniya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China