Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Karo Na Hudu Ne An Gudanar Da Atisayen Gwajin Shirye-Shiryen Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2020
2020-01-21 11:30:39        cri

A dab da bikin bazara na dukkanin al'ummar kasar Sin dake gida da waje, a jiya Litinin, an kammala atisayen gwaji na hudu na bikin murnar bikin bazara da babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG zai gabatar. Cikin shirye-shiryen kide-kide da raye-raye na bikin, an bayyana walwalar rayuwar al'ummomin kasar Sin. Kuma a wasu shirye-shiryen raye-raye, an maida hankali kan rigar mata ta gargajiyar kasar Sin wato Qipao, yayin da kuma aka hada harkokin gargajiya da na zamani tare, wadanda suke da ban sha'awa kwarai da gaske. Haka kuma, an hada shirin raye-raye da mutum-mutumin inji masu fasahohin zamani tare, lamarin da ya zama tamkar cikin mafarki.

Bugu da kari, shirye-shiryen wasan magana cikin raha na bikin sun bada dariya kwarai da gaske, wadanda baya ga nuna harkokin zaman rayuwa ba, suka kuma nuna kwarewar 'yan wasan.

A ranar 24 ga wata, za a watsa bikin a hukumance, dandalin bikin dake birnin Beijing zai yi hadin gwiwa da dandalin da aka kafa birnin Zhengzhou na lardin Henan, da ma dandalin aka kafa a babban sashen mashigin teku na Guangdong-Hong Kong-Macao, wato GBA, domin gabatar da wani biki mai kyau ga dukkanin al'ummomin duniya. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China