Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta nada babbar darektar UNON
2019-12-31 09:13:08        cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya sanar da nada Zainab Hawa Bangura 'yar kasar Saliyo a matsayin babbar darektar ofishin MDD dake Nairobin kasar Kenya(UNON).

Wata sanarwa da MDDr ta fitar ta bayyana Bangura a matsayin mai fafatukar daidaita da rikicin da sasantawa kana mai ragin kare hakkin bil-Adam. Kafin wannan matsayi, jami'ar ta rike mukamin wakilar babban sakataren MDD ta musamman kan cin zarafin jinsi yayin tashin hankali, mukamin da ta rike daga shekarar 2012 zuwa 2017.

Haka kuma ta taba rike mukamin ministar lafiya da tsaftar muhalli, da ministar harkokin kasashen waje da hadin gwiwar kasa da kasa a gwamnatin kasar Saliyo.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China