Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Najeriya ya lashi takwabin daukar matakan kawar da talauci
2020-01-02 10:30:18        cri
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya lashi takwabin ci gaba da aza harhashin da ya dace a shekarar 2020, don fitar da 'yan kasar miliyan 100 daga kangin takauci a cikin shekaru goma masu zuwa.

Shugaban wanda ya bayyana hakan cikin jawabinsa na murnar shiga sabuwar shekara ta 2020 ga 'yan kasar, ya ce, gwamnatinsa za ta samar da sabbin damammaki a muhimman sassa a sabuwar shekara, don magance kalubalen talauci da 'yan kasar ke fuskanta.

Idan ba a manta ba, yayin da shugaban ke kaddamar da majalisar ba da shawara kan tattalin arziki mai mambobi 8 a watan Oktoban shekarar 2019 da ta shude a Abuja, fadar mulkin kasar, ya umarci majalisar da ta zage damtse wajen ganin an fitar da 'yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci a cikin shekaru 10.

Ya ce, duk da cewa, kasar ta fita daga karayar tattalin arziki a shekarar 2017, amma yadda tattalin arzikin kasar ke bunkasa, bai kai ga biyan bukatun burin makomar kasar ba.

Alkaluman nazarin talauci na duniya na shekarar 2019 na nuna cewa, akwai 'yan Najeriya da yawansu ya kai miliyan 93.7 dake cikin kangin talauci, adadin da ya dara na shekarar 2018, wato miliyan 6.8. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China