Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin ya yi hira da masu yawon shakatawa a Yunnan
2020-01-20 11:22:04        cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya yi rangadin aiki a garin Heshun a birnin Tengchong na lardin Yunnan da ke kudu maso yammacin kasar, da yammacin jiya Lahadi.

Yayin da yake yawo a titin dake garin Heshun, wata mai yawon shakatawa ta yi masa tambayar ba-zata, inda ta ce "Ina uwargida take?" Shugaba Xi Jinping ya yi murmushi, yana mai amsa mata cewa, Uwargida ba ta zo ba, domin akwai ayyuka da yawa a gida gabannin bikin bazara. Da jin haka, sai dukkan wadanda ke wurin suka yi murmushi. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China