Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Aung San Suu Kyi: Makomar bai daya ta hada Sin da Myanmar
2020-01-18 00:35:32        cri
A yau Jumma'a a birnin Naypyidaw, fadar mulkin kasar Myanmar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugabar gwamnatin kasar ta Myanmar, Madam Aung San Suu Kyi. A yayin ganawar, Madam Aung San Suu Kyi ta ce, 'yan uwantakar da ke tsakanin kasashen biyu ta jure sauye-sauyen yanayi, kuma mu kadai ke fahimtar ma'anarta. Kullum kasar Sin babbar kawa ce ta Myanmar, kuma makomar bai daya ta hada mu.

A nasa bangaren, shugaba Xi Jinping ya ce, Sin na nuna goyon baya ga Myanmar da ta bi hanyar da ta zaba, kuma tana fatan kara inganta 'yan uwantaka a tsakanin kasashen biyu da ma al'ummarsu, don samar da kyakkyawar makoma ta bai daya ga kasashen biyu.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China