Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: Ya kamata a raya zirin tattalin arziki tsakanin Sin da Myanmar don kara samar da alheri ga jama'a
2020-01-18 17:36:20        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yau Asabar a Naypyidaw na kasar Myanmar cewa, raya zirin tattalin arziki tsakanin Sin da Myanmar, muhimmin aiki ne dake gaban kasashen biyu, a kokarin da suke na raya shawarar "Ziri daya da hanya daya". Ya ce yanzu bangarorin biyu sun riga sun soma ayyukan raya zirin tattalin arziki a tsakaninsu, da nufin kara samar da alheri ga jama'ar kasashen biyu, musamman ma ga jama'ar kasar ta Myanmar.

A wannan rana kuma, Xi Jinping ya gana da shugabar gwamnatin kasar Myanmar Aung San Suu Kyi, kana sun halarci bikin musayar takardu game da hadin kan bangarorin biyu a fannonin da suka shafi siyasa, tattalin arziki da cinikayya, zuba jari, al'adu da dai sauransu. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China