Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Myanmar sun bude sabon zamanin huldar da ke tsakaninsu
2020-01-18 17:30:39        cri
A yau Asabar a birnin Naypyidaw, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugabar gwamnatin kasar Myanmar Aung San Suu Kyi. A sanarwar hadin gwiwa da kasashen biyu suka fitar, sun amince da gina al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya a tsakaninsu tare da bude sabon babi ga huldar da ke tsakaninsu, a daidai lokacin da kasashen ke cika shekaru 70 da kulla huldar diplomasiyya.

A yayin shawarwarin, Madam Aung San Suu Kyi ta bayyana cewa, wata sigar musamman ta huldar da ke tsakanin Sin da Myanmar ita ce fahimta da martabawa da kuma tallafawa juna. Ta ce kasar Sin tana goyon bayan Myanmar ne ba tare da son kanta ba, sannan tana tabbatar da adalci da gaskiya. Ta kara da cewa, wasu kasashe na tsoma baki cikin harkokin gidan wasu kasashe bisa dalilai na kare hakkin bil Adam da kabilu ko kuma addini, abin da ko kadan Myanmar ba za ta yarda da shi ba. Tana kuma fatan Sin za ta ci gaba da kiyaye moriyar kananan kasashen da suka hada da Myanmar a harkokin kasa da kasa.

A nasa bangaren, shugaba Xi Jinping ya ce, har kullum, kasar Sin na martaba al'ummar kasa da kasa bisa zabar hanyoyin da suka dace da yanayin da suke ciki, kuma tana tsayawa kan rashin tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashe, sannan, tana kuma goyon bayan Myanmar a kokarin da take na kiyaye martabar kasa da kuma hakkinta.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China