Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bankin duniya ya rage hasashensa na ci gaban tattalin arzikin duniya, sai dai bai sauya hasashensa dangane da na kasar Sin ba
2019-06-05 13:28:16        cri
Bankin duniya ya rage hasashensa na ci gaban tattalin arzikin duniya a 2019 zuwa kaso 2.6, sai dai, hasashensa dangane da ci gaban tattalin arzikin kasar Sin na nan akan kaso 6.2.

A cewar rahoton hasashen tattalin arzikin duniya da bankin ke fitarwa sau 2 a shekara, karuwar manufofi na rashin tabbas, ciki har da ta'azzarar takaddamar cinikayya tsakanin kasashe masu karfin tattalin arziki, ya janyo raguwar kwarin gwiwa da zuba jari a duniya.

Rahoton ya ce an sake nazarin ci gaban harkokin cinikayya a duniya na bana, inda ya sauka kasa da kaso daya cikakke zuwa kaso 2.6, wanda ya kasance mataki mafi karanci tun bayan matsalar hada hadar kudi ta duniya.

Daraktan ayarin masu hasashe na bankin duniya Ayhan Kose, ya ce akwai yiwuwar a rage hasashen kaso 2.7 da aka yi na ci gaba tattalin arzikin duniya a shekarar 2020 da kaso daya zuwa kaso 1.7 idan takaddamar cinikayyar ta ci gaba da ta'azzara.

Sai dai a cikin rahoton, bankin duniyan bai sauya hasashen kaso 6.2 da ya yi na ci gaban tattalin arzikin kasar Sin a bana ba, ya na mai bada misali da raguwar cinikayya a duniya da tsayayyen farashin kayayyaki da ingantaccen yanayin hada-hadar kudi na duniya da kuma karfin hukumomi na amfani da managartan dabarun hada-hadar kudi da na kasashe kashe da kudin shigar gwamnati wajen magance kalubalen da za a fuskanta. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China