Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban bankin duniya ya yabawa ci gaban Sin wajen yaki da fatara
2019-10-18 10:46:34        cri

A yayin da ake bikin ranar yaki da talauci ta duniya, shugaban bankin duniyar David Malpass ya ce, sakarwa kasuwa mara a harkokin tattalin arzikin Sin a wasu gomman shekaru da suka gabata, ya taka gaggarumar rawa wajen fitar da daruruwan miliyoyin mutane daga kangin talauci.

Malpass ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da yake amsa tambayar da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya yi masa, a taron manema labarai na taron karawa juna sani na shekara shekara na bankin duniya da asusun ba da lamuni na IMF na shekarar 2019.

Babban jami'in bankin duniyar ya bukaci kasar Sin da ta ci gaba da yin sauye sauye a bangaren kasuwa, da karfafa dokoki, domin kara karfafa karfin gogayya na kamfanonin dake mallakar gwamnatin kasar, wadanda ke da matukar muhimmanci wajen bunkasa ci gaban tattalin arzikin kasar, da kara yakar fatara a kasar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China