Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Karamin ofishin jakadancin kasar Birtaniya ya ce shi da kansa ne ya bukaci 'yan sandan yankin Hong Kong su kama masu zanga-zanga
2020-01-15 14:47:47        cri
A jiya Talata, wani shafin yanar gizo dake goyon bayan yin zanga-zanga tare da nuna karfin tuwo a yankin Hong Kong na kasar Sin ya nuna wata sanarwar da karamin ofishin jakadancin kasar Birtaniya dake Hong Kong ya gabatar, inda ofishin ya amince cewa, shi da kansa ne ya fadawa 'yan sandan Hong Kong yiwuwar abkuwar aikace-aikacen keta doka a kusa da ofishin a kwanaki biyu da suka wuce, lamarin da yasa 'yan sanda suka isa wurin tare da kama wasu mutane, ciki har da wata yarinya mai shekaru 15 a duniya.

Kafin gabatar da sanarwar, ko da yake 'yan sandan yankin Hong Kong sun ce sun dauki matakin ne bisa bukatar karamin ofishin jakadancin kasar Birtaniya, amma duk da haka, wasu kafofin yada labarai na kasar Birtaniya, ciki har da jaridar the Thames, sun dauki maganar wai "masu fafutukar kare hakkin dan Adam", da wasu 'yan siyasan kasar Birtaniya, inda suka soki lamirin 'yan sandan Hong Kong kan yadda suka "kutsa kai" cikin karamin ofishin jakadancin Birtaniya don kama "masu zanga-zanga". Yayin da a hakika wadannan mutane masu ta da kayar-baya ne dake neman ballewar yankin Hong Kong daga kasar Sin. A lokacin, wani mamba mai kula da hakkin dan Adam ta jam'iyyar Conservative Party ta kasar Birtaniya, mai suna Luke de Pulford, ya watsa wani bayanin da aka rubuta a shafinsa na sada zumunta, inda aka bayyana aikin 'yan sandan Hong Kong a matsayin "aikin ta'addanci".

Amma yanzu wannan sabuwar sanarwar karamin ofishin jakadancin kasar Birtaniya ta bata fuskar wadannan kafofin watsa labaru da 'yan siyasa na kasar Birtaniya. Yanzu Luke de Pulford da 'yan ta da kayar-baya na Hong Kong, gami da masu goyon bayansu, dukkansu suna kokarin nuna yatsa ga karamin ofishin jakadancin Birtaniya dake Hong Kong, wai ofishin ya "ci amanarsu". (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China